Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

28 Afirilu 2022

22:06:33
1252811

Tattalin Arzikin Jamhuriyar Nijar Yana Samun Bunkasa A Cikin Shekarun Bayannan

A sanarwar bayan taro na majalisar ministocin kasar, an bayyana cewa: Daga shekarar 2011 zuwa 2020 tattalin arzikin kasar ta Nijar ya samu bunkasa da kaso 6%.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar ta ci gaba da cewa; Al’ummar kasar za su ga sakamakon wannan ci gaban, idan har aka yi aiki da tsarin kayyade iyali.

Bayanin ya ci gaba da cewa; A hakikanin gaskiya ci gaba da haife-haife a cikin al’umma, zai hana iyalai yin tsumi da tanadi, bisa la’akari da kruwar yawan samari, da hakan yake sanya daukar nauyinsu ya yi tsauri.

Har ila yau, bayanin ya ambato wani rahoto na Bankin Duniya wanda ya yi ishara da hatsarin lafiya ga yara da iyaye mata, da yake tattare da yawan haihuwa, a karshe kuma hakan yake barazana ga bunkasa rayuwar mutane da kuma bunkasar tattalin arziki.

Wani sashe na sanarwar ya tabo batun sauyin yanayi da karancin saukar ruwan sama da kuma raguwar ruwan karkashin kasa tun a 1970’s, da hakan ya sa gwamnati mayar da hankali wajen samar da madatsan ruwa.

342/