Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

28 Afirilu 2022

22:05:54
1252810

Rasha: Aikewa Da Makamai Zuwa Kasar Ukiraniya Yana Yin Barazana Ga Tsaron Nahiyar Turai

Fadar shugaban kasar Rasha Kremlin ta bayyana cewa; Yadda kasashen turai su ke ci gaba da aikawa da makamai zuwa kasar Ukiraniya, yana a matsayin barazana da hastari ga tsaron nahiyar tasu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin fadar mulkin kasar ta Rasha Dmitry Peskov ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani akan fururcin da ministar harkokin wajen Birtaniya ta yi na wajabcin aikewa da manyan makamai zuwa Ukiraniya, Goergia da kuma Maldova domin kalubalantar Rasha.

Peskov ya ci gaba da cewa; Abinda kasashen turai din suke yi zai kuma jefa nahiyar cikin rashin tabbaci.

A wani gefen sojojin kasar ta Rasha suna ci gaba da kai hare-hare a kasar Ukiraniya, inda a cikin sa’oi 24 su ka kai hari akan cibiyoyi 67 na soja.

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ce ta sanar da kai hare-haren na yau, wanda ya ce ya shafi bangarori daban-daban na soja da wuraren bayar da horo.

Har ila yau, ma’aikatar tsaron ta Rasha ta sanar da kashe mayakan Ukiraniya da take kira ‘yan Nazi 300 da kuma lalara motocinsa 40.

342/