Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

28 Afirilu 2022

22:03:11
1252807

Putin : Duk Kasar Data Shiga Yakin Ukraine Za Ta Gane Kurenta

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin daukar matakin gaggawa na soja kan duk wata kasa da ta tsoma baki a aikin sojan da kasarsa ke yi a Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake jawabi ga 'yan majalisar dokokin Rasha a ranar Laraba, Putin ya ce "idan wani ya yi gigin haifar mana da barazana da ba za a yarda da ita ba, ‘’martaninmu, zai kasance cikin sauri.”

Shugaban ya ce sojoji ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da makamanmu na zamani, Kuma ina son kowa ya san hakan.”

Kalaman na Putin na zuwa ne bayan taron Jamus, na kasashen yamma da Amurka inda sukayi alkawarin ci gaba da baiwa Ukraine makamai.

Kafin hakan dama ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi gargadi game da hadarin da ke tattare baiwa Ukraine karin makamai, wanda zai iya haifar da yakin duniya na uku.

342/