Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

28 Afirilu 2022

22:02:32
1252806

Mali : Hukumar Koli Ta Sadarwa Ta Amince Dakatar Da Rfi Da F24

Hukumar koli ta sadarwa a Mali, ta amince da rufe gidan radiyon Rfi da kuma tashar talabijin ta faransa F24 daga watsa shirye shiryensu kwata kwata a fadin kasar.

Tun ranar 17 ga watan Maris da ya gabata ne hukumomin Mali suka bayar da umarnin rufe kafofin yada labaren guda biyu.

A sanarwar da ta fitar kwanan baya Gwamnatin Mali ta bada umarnin rufe gidan radiyon faransa rfi da kuma tashar talabijin ta france24 har sain abunda hali ya yi.

Sannan an haramtawa duk wata kafa ta kasar Malin, watsa shirye shiyen wadanan tashoshin a cikin gida.

Malin dai na zarginsu da yada labarai marar tushe da kuma na neman batawa sojojin kasar da mahukuntan rikon kwaryar soji suna.

A martanin da ta fitar hukumar kula da kafofin yada labaren kasar ta faransa, France Médias Monde, ta kalubalanci matakin da cewa marar tushe sannan kuma zatayi amfani da duk hanyoyin da suka dace domin kalubalantar matakin, da kuma nemo hanyoyin ci gaba da sanar da ‘yan Malin halin da duniya ke ciki.

342/