Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

28 Afirilu 2022

22:00:57
1252804

AfDB: Farashin Alkama Zai Karu Da Kaso 60% A Afirka

Shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwunmi Adesina, ya ce rikicin Rasha da Ukraine, zai haddasa hauhawar farashin alkama da kusan kaso 60 bisa dari a kasashen nahiyar Afirka.

M. Adesina ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, a fadar gwamnatin kasar dake birnin Abuja, Inda ya ce, tashin hankalin ya haifarwa duniya tarin kalubale, musamman ma kasashen Afirka, masu shigo da kaso mai yawa na abincin da suke bukata daga kasashen biyu.

Adesina wanda tsohon ministan ma’aikatar noma ne a Najeriya, ya ce a daminar bana, bankin AfDB zai taimakawa kananan manoman Najeriya a kalla miliyan 5, ta yadda za su iya noman hekta miliyan 1 ta masara, da hekta miliyan 1 ta shinkafa, da hekta 250,000 ta dawa da waken soya.

342/