Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

27 Afirilu 2022

18:46:39
1252407

Yan Adawa A Kasar Tunusiya Sun kulla Wani Sabon Kawance

Fitaccen dan siyasar nan na kasar Tunusiya shi ne ya sanar da kafa sabon kawancen domin daidaita kundin tsarin mulki a kasar bayan da shugaban kasar Kais said ya kwace iko da madafun ikon kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Idan ana iya tunawa a shekata ta 2019 ne aka zabi sabon shugaban kasar kuma ya rusa gwamnatin kasar a ranar 25 ga watan yulin shekara tat a 2021 da ta gabata, abin da yan adawa suka kira da juyin mulki

Anasa bangaren Ahmed Najib Chebbi ya sanar cewa mun kafa sabon kwance ne don ceton kasa mai suna national Salvation Front , kawancen siyasa ne da ya kunshi jami’iyun siyasa 5 da ya hada da gungun yan majlasa guda 6, yace wannan so mi tabi ne muna so mu ci gaba da tattaunawa da sauran Jamiyun siyasar kasar domin shiga cikin kawancen.

Haka zalika sabon kawance ya hada da Jam’iyu guda 5 ciki har da ta masu kishin Addinin ta Annahdha da kuma wasu kungiyoyin farar hula guda 5 da wasu fitattun yan siyasa masu zaman kansu.

A watan yuli ne za’a kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a a kasar ta Tusnuiya kafin zaben yan majalisu a watan Decemba mai zuwa.

342/