Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

27 Afirilu 2022

18:44:26
1252405

Daliban Jami'a A Najeriya Sun Koka Kan Yadda Aka yi Watsi Da Halin Da Suke ciki.

Wannan yana zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriya da jami'an kungiyar malaman jami'a ta kasar ASUU suka kasa cimma wata matsaya kan warware rikicin da ya janyo malaman suka tsunduma cikin yajin aiki tun cikin watan Fabrairun d aya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban kungiyar malman jami’oi ta ASUU Farfesa Victor Emmanuel Osodeke ya shaida wa manema labarai cewa gwamnati ta yi watsi da batun tattaunawar da bangarorin biyu ke yi. kuma gwamnatin ta daina nemansu, har ta kai ga ta fara hana su albashi tsawon wata biyu ke nan.

Har ila yau Farfesan ya ce hana su albashinsu ba zai sa gwuiwoyinsu su yi sanyi ba, kuma za su ci gaba da fafutukar da suek yin a neman hakkokinsu. Yace “A bara ma an hana mu albashinmu na wata takwas zuwa tara kuma ba mu mutu ba."

Kungiyar ASUU ta ce ta tsunduma cikin yajin aikin ne saboda gwamnatin Najeriya ta ki biyan 'ya'yan kungiyar wasu hakkokinsu, a karkashin wata yarjejeniya da suka kula tun shekarar 2009 tsakaninsu.

342/