Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

27 Afirilu 2022

18:37:21
1252399

​Putin: Matsalar Ukraine Ta Fara Ne Tun Daga Lokacin Kawar Da Halastacciyar Gwamnati A 2014

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, matsalar kasar Ukraine ta fara ne tun daga lokacin da sabbin ‘yan Nazy suka kifar da halastacciyar gwamnati a kasar a cikin shekara ta 2014.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Putin ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres a jiya a fadar Kremlin a birnin Moscow fadar mulkin kasar ta Rasha.

Guterres ya bayyana damuwarsa matuka dangane da halin da ake ciki a kasar Ukraine, musamman ma a bangaren ayyukan agaji da jin kai a birnin Mariupol, inda ya ce ayyukan sun tsaya cak.

Sannan kuma ya jaddada bukatar dakatar da bude wuta domin samun damar gudanar da ayyukan jin kai da kuma fitar da fararen hula daga wurare masu hadari.

A nasa bangaren shugaba Putin ya shedawa babban sakataren na majalisar dinkin duniya cewa, rahotannin da ake ba shi kan ayyukan jin kai ba gaskiya ba ne, musamman kan batun birnin Mariupol, domin kuwa a cewarsa Rasha ta fitar da fararen hula kimanin dubu 140 daga birnin tare da ba su kulawa, amma matsalar ita ce fararen hula wadanda sojojin Ukraine suka hana su fitowa, suna amfani da hakan a matsayin wani makami na siyasa.

Putin ya ce Rasha ba ta bukatar yaki, amma kare kanta ya zama wajibi, domin kuwa babu wata kasa ta duniya da za ta bari wasu su yi amfani da wata kasa domin a rusa ta, ko a haifar mata da barazana ta tsaro, wanda zai iya shafar makomar al’ummarta.

342/