Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

26 Afirilu 2022

19:16:40
1252069

Kasar Faransa Za Ta Harbawa Najeriya Taurarin Dan Adam 20 A Sarrin Samaniya

Kafar watsa labaru ta “ Africa Intelligence” ta bayar da labarun cewa; Kamfanin sanawa na kasar Faransa Promethee ne zai harba taurarin dan adam din a madadin Nigeria har guda 20.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin watan Mayu mai zuwa ne dai ake sa ran cewa ministan kimiyya na Nigeria Ogbonnaya Onu zai wakilci kasarsa wajen rattaba hannu a harjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Promethee akan shirin na harba taurarin dan’adam din.

Taurarin da za a harba dai za su mayar da hankali ne wajen tattara bayanai dangane da harkokin tsaro da sanya ido akan iyakokin kasar.

342/