Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

26 Afirilu 2022

19:06:29
1252058

Sudan : An Tura Sojoji Domin Dakile Fadan Kabilanci A Darfour

Hukumomi a Sudan sun ce sun kara tura dakaru zuwa yammacin yankin Darfur domin taimakawa wajen dakile fadan kabilanci da ya lakume rayukan mutane sama da 175 a cikin kwanaki biyar da suka gabata, kamar yadda jami'ai da kungiyoyin agaji suka sanar a jiya Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan tsaro Maj. Gen. Yassin Ibrahim Yassin ya ce sun karfafa tsaro a lardin tare da tura dakaru domin raba bangarorin da ke fada da juna.

Fadan ya barke ne tsakanin Larabawa da kabilar Masalit ta Afirka a ranar Lahadi a garin Kreinik mai tazarar kilomita 80 daga gabashin babban birnin lardin Genena.

Kafin hakan bayanai sun ce hukumomi sun ayyana dokar hana fitar dare a yankin domin taimakawa dalike rikicin.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres yayi Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan kisan wasu Larabawa biyu da wasu mahara suka yi a lardin Kreinik ranar Alhamis.

Akalla mutane 168 ne suka mutu, yayin da wasu 89 suka jikkata a ranar Lahadin da ta gabata kadai, a cewar kungiyar kula da 'yan gudun hijira a yankin Darfur, kana kuma a ranakun Alhamis da Juma'a mutane 8 sun mutu a rikicin wasu kuma 16 suka jikkata, in ji sanarwar.

342/