Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

25 Afirilu 2022

17:36:56
1251666

Zazzabin Malaria Na Barazana Ga Rabin Al’ummar Duniya

Yau 25 ga watan Afrilu, ita ce ranar da MDD, ta ware domin yaki da zazzabin cizon sauro ko malaria.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahoton da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa rabin al’ummar duniya na fuskantar barazanar zazzabin na Malaria.

Kuma a rahoton da ta fitar hukumar ta ce a shekarar 2020 mutum miliyan 241 ne suka kamu da zazzabin cizon sauro a fadin duniya kuma 627 000 zazzabin ya kashe a kasashe 85.

Sannan mafi akasarin wadanda lamarin ya shafa sun kasance ne a nahiyar Afrika inda dubban yara suke mutuwa a ko wacce shekara.

A cewar hukumar ta WHO, karuwar cutar a cikin watanni 12 da suka gabata, ya faru ne sanadin hargitsin da aka samu mai nasaba da annobar cutar korona.

Domin rage tasirin zazzabin, hukumar ta ce an samar da magunguna na riga kafi ga mata masu juna biyu da kuma jarirai dake rayuwa a wuraren dake da hadarin zazzabin dama kuma masu balaguro.

342/