Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

25 Afirilu 2022

17:32:20
1251661

​London: Wasu Yahudawa Sun Kona Tutar Isra'ila A Gaban ofishin Firaminista

An kona tutar gwamnatin Isra’ila a gaban ofishin firaministan kasar Birtaniya a ranar jiya Lahadi a karshen wani tattakin nuna goyon baya ga al’ummar al’ummar falastinu a birnin London.

Malaman addinin yahudawan da ke nuna adawa da wanzuwar gwamnatin sahyoniyawa sun kona tutar gwamnatin Isra’ila a gaban ofishin firaministan Birtaniya a birnin landan.

Ta haka ne suka bayyana matsayinsu na nuna adawa da laifukan yaki da wannan gwamnati take aikatawa, musamman abubuwan da suka faru a masallacin Aqsa.

Al-Henan Beck daya daga cikin malaman addinin yahudawan da suka shiga zanga-zangar ya ce mafita daya tilo da za a magance rikicin Falasdinu da Isra'ila shi ne kawar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.

Masu zanga-zangar sun yi maci a tsakiyar birnin Landan, gaban majalisar dokokin Birtaniya da ofishin harkokin wajen kasar, sannan suka taru a kofar ofishin Firayim Minista.

Sun rera taken nuna adawa da Isra'ila suna kira da a kawo karshen mamaya da tashe tashen hankula da nuna wariya a Falasdinu da ta mamaye.

Wasu masu magana da kuma masu adawa da Isra'ila a Biritaniya su ma sun yi Allah wadai da laifukan da ake tafkawa a Palastinu da Isra’ila ta mamaye tare da yin kira da a kara matsin lamba na kasashen duniya kan dakatar da ayyukan yaki haramtacciyar kasar Isra'ila musamamna birnin Quds.

342/