Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

25 Afirilu 2022

17:31:01
1251660

​Najeriya: Buhari Ya Yi Umarni Da A Kamo Masu Haramtacciyar Matatar Man Fetur

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro, musamman wadanda ke da kware wa da su bankado tare da cafke wadanda ke daukar nauyin gudanar da ayyuka a haramtacciyar matatar mai a Imo.

Haramtacciyar matatar man wadda ta janyo mutuwar mutane sama da 100 a ranar juma’ar da ta gabata a karamar hukumar Ohaji-Egbema da ke Jihar Imo.

Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne cikin wata sanarwar da Babban Mai Taimaka masa na musamman a harkar yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar a garin Abuja.

Buhari ya danganta iftila’in a matsayin babbar annobar da ta shafi kasa baki daya, inda ya bayyana cewa, cafko masu dukar nauyin matatar wacce ta janyo mutuwar jama’a da dukiyoyi abu ne da ya zama wajibi, don su fuskanci Shari’a.

Shugaban Buhari ya kuma jajanta wa ‘yan uwa da alumar Jihar da kuma Gwamnatin jihar ta Imo bisa faruwar lamarin.

342/