Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

23 Afirilu 2022

18:42:34
1250944

Bayanin "Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya" Dangane Da Sabbin Ta'addancin Yahudawan Sahyuniya Da Suka Aikata A Masallacin Al-Aqsa.

Ta yaya gwamnatin sahyoniyawa ke cigaba da cin zarafi tare da wulakanta wurin ibada da mala'iku suke sauka! Kuma ba wai kawai babu wata murya daga gwamnatocin Musulunci ba da zasu kwabe su ba, a'a har yanzu wasu shugabannin Larabawa suna tunanin daidaita dangantaka da wannan Lalatacciyar hukuma?!

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, bayan sabbin laifukan da yahudawan sahyuniya suka aikata a yankunan da suka mamaye da kuma wulakanta masallacin Al-Aqsa, Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya fitar da bayanin yin tir da wadannan ayyuka.

Cikakken bayanin wannan bayani shi ne kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

«سُبحَانَ الَّذِي أسْرىٰ بِعَبدِهِ لَيلًا مِنَ المَسجِدِ الحَرَامِ إِلَى المَسجِدِ الأقصَى الَّذي بارَكنا حَولَه...».

Watan Ramadan wata ne da al’ummar Musulman duniya suka fi maida hankali kan masallatai da ibada da karatun Alkur’ani da addu’o’i. Su ma masu imani da sauran addinai sun girmama tarr yaba da jajircewar da musulmi suka yi wajen gudanar da ibada a cikin wannan wata, wasu ma har tare da musulmi suke daukar azumin.

Amma gwamnatin sahyoniya mai muguwar dabi’a wacce baya ga kauracewa da dokokin Ubangiji, ba ta jin ko da kamshin dan’adam da jin kansa, tana barin hannun ‘yan cin zarafi a bude, kuma a duk shekara a cikin wannan wata, suna wulakanta daya daga cikin wurare mafi tsarki na addinan cikin duniya

Kudus mai tsarki ba wai ga musulmi kadai ba ne, har ma da mabiya sauran addinai na Ibrahim, kuma masallacin Al-Aqsa - a matsayin alkiblar musulmi ta farko da yin Mi'iraji da Manzon Allah (SAW) - daga nan ne, ya kasance yana haskakawa kamar jauhari a cikin wancan birni mai tsarki.

To, ta yaya ne gwamnatin sahyoniyawan da ke cin karenta ba babbaka take yi wa wannan guri na hawa da saukar mala'iku rashin daraja; Kuma ba wai kawai babu wata murya daga gwamnatocin Musulunci ba da zata kira da dena hakan ba, a a har takai yanzu wasu shugabannin Larabawa suna tunanin daidaita dangantaka da wannan lalaracciyar gwamnati?! Kuma me ya sa kungiyoyin kasa da kasa da suke daukar kansu a matsayin masu kare hakkin bil'adama da ake tauyewa, ba sa yin aikinsu wajen fuskantar wadannan laifuka na cin zarafin bil'adama?!

Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya - a matsayinta na kungiyar kasa da kasa wadda daruruwan masu fada a ji na kasashen musulmi suke cikinta - tana yin Allah wadai da abubuwan da suke faru a masallacin Al-Aqsa na baya-bayan nan tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta da kuma Gwagwarmayar su.

Majalisar ta kuma yi kira ga mambobinta, da sauran masu fada aji a addinai, malamai da masu tunani na kasashen musulmi, masu 'yanci na duniya, kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kungiyoyin zaman lafiya, da su kare alfarmar wurare masu tsarki da kuma goyon bayan al'ummar Palastinu da ba su da kariya. ta hanyar yin Allah wadai da zaluncin ‘yan mamaya.

Babu shakka, ƙarshen tsayin daka shine nasara, kuma a ƙarshe zalunci da ta'addanci shine shan azabar Ubangiji mai raɗaɗi.

«تِلْكَ الدَّارُ الآخِرَةُ نَجعَلُهَا لِلَّذِينَ لا يُريدونَ عُلُوًّا في الأرضِ وَلا فَسادًا وَالعاقِبَةُ لِلمُتَّقين».

Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya
21 Afrilu, 1401