Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

23 Afirilu 2022

18:39:08
1250942

Bayanin Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Na Yin Tir Da Cin Mutuncin Kur'ani Miai Tsarki A Kasar Sweden.

Wadannan hanyoyin yada kiyayya da tunzura jama'a na addini suna haifar da kiyayya da rarrabuwar kawuna a cikin al'ummomin bil'adama da cin mutuncin kimar 'yanci da ra'ayoyin dan'adam kuma hakan maslahar masu tsattsauran ra'ayi kawai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, bayan batancin da wasu masu tsattsauran ra'ayin addini a kasar Sweden suka yi wa Alkur'ani mai tsarki, Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ta fitar da wani bayani wanda acikinsa da ta yi Allah wadai da wannan danyen aikin da suka aikata.

Cikakken bayanin wannan bayani shi ne kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Cin rafin da daya daga cikin jam'iyyun siyasar kasar Sweden tayi na cin mutuncin kur'ani mai tsarki ya cutar da zukatan dukkanin musulmi da 'yantattun mutane; Haka nan kuma a cikin watan Ramadan mai alfarma, inda da yawa daga cikin mabiya sauran addinai su ma suke nuna goyon bayansu ga musulmi tare da girmama imaninsu da ayyukansu.

Ba za a iya jurewa ko rufe bakin zaren wannan hari da aka kai kan akidar mutane kusan biliyan biyu da cin mutuncin addininsu da littafin Allah ba. Wannan aiki maimaituwa ne akan na baya-bayanan na yunƙurin nuna ƙyama da ƙiyayya - kamar zana zane-zane da fina-finai na cin mutuncin ga Manzon Allah (SAW) da Ya gabata.

Irin wannan ayyuka na rashin hankali da tsaurin ra'ayi, yunkuri ne na nuna wariyar launin fata da kyama wadanda baya ga tunzura al'ummar musulmi, suna haifar da kiyayya da tashin hankali da kuma jefa yunkurin da ake yi na neman zaman tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya cikin hatsari.

Wadannan hanyoyin yada kiyayya da lalata ra'ayoyin addini suna kunna wutar fushi da rarrabuwar kawuna a cikin al'ummomin bil'adama, da cin mutuncin kimar dan Adam da ra'ayoyin 'yanci, kuma suna cikin muradun masu tsattsauran ra'ayi ne kawai da mutane masu son tashin hankali.

Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya a yayin da take yin Allah wadai da wannan mummunan mataki na rashin mutuntaka, ta yi kira ga gwamnatin kasar Sweden da majalisar dokokin kasar da su hukunta Masu cin mutuncin imani da littafan addinai ta hanyar fitar da wata doka da kuma hana sake aukuwar irin wannan lamari. .

Ya kamata gwamnatin Sweden da sauran ƙasashen Turai su gane kuma su tabbatar da wannan ƙa'idar a bayyane cewa Karara babu wani addini na allahntaka da za a iya zagi a ƙarƙashin sunan "'yancin faɗar albarkacin baki".

Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta Duniya

21 Junairu 2022