Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

23 Afirilu 2022

18:31:48
1250933

Guteress Zai Ziyarci Rasha Da Ukraine, Da Nufin Dakatar Da Yaki

Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da cewa babban sakatarenta, Antonio Guterres, zai ziyarci kasar Rasha a ranar Talata mai zuwa, inda zai gana da shugaba Vladimir Putin da kuma ministan harkokin wajen Rashar Sergio Lavrov.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan ziyara a cewar sanarwar da ofishin MDD, ya fitar na da zummar tattaunawa da mahukuntan Rasha a wani yunkuri na kawo karshen yakin da Moscow ta kaddamar kan Ukraine.

Haka kuma babban sakataren na MDD, zai isa birnin Kiev, na Ukraine inda zai gaba da shugaba Volodymyr Zelensky, duk da dai a makon mai zuwa.

Zai tattauna da dukkan bangarin da abunda ake ganin zai iya kawo zaman lafiya cikin gaggawa a Ukraine a cewar kakakin MDD Eri Kaneko.

A yau dai asn shiga kwana na 58 na matakin sojin da kasar Rasha ta ce ta dauka kan Ukraine.

Kuma tattaunawar da ake tsakanin bangarorin da nufin kawo karshen yakin ta gaza har kawo yanzu.

024