Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

23 Afirilu 2022

18:29:01
1250929

​Sweden: An Kori Wata ‘Yar Jarida Daga Gidan Talabijin Na Kasa Kan Adawa Da Kona Kur’ani

Gidan Talabijin na kasar Sweden ya kori wata ‘yar jarida mai sukar dan siyasar da ke cin mutuncin musulmi da keta alfarmar kur'ani mai tsarki, bisa hujjar cwa ‘yar jaridar ta nuna rashin kishin kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin tashar Tashar Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan gidan talabijin na kasar Sweden sun yanke shawarar korar wannan ‘yar jarida ne kuma ma’aikaciyar tashar, saboda matsayarta a kan lamarin kona kur’ani a kasar.

Anton Asundsen daraktan bangaren labarai na tashar STV ya ce sun kammala dukkanin bincike kan wannan lamari, kuma sun kai ga sakamakon cewa wannan ‘yar jarida ba ta kiyaye ka’aidar aikinta ba wajen daukar matsakaicin ra’ayi,a kan hakan sun yanke shawarar korar ta daga aiki baki daya.

‘Yar jaridar dai ta sokin Rasmus Paludan nea lokacin da take zantawa das hi, kan kona kur’ani da ya yi.

A jawabin da ya yi a birnin Gothenburg na kasar Sweden, inda musulmi da dama ke zaune, Paludan ya ci zarafin addinin musulunci da kuma manzon Allah (SAW) da gangan.

Kasashe da dama da suka hada da Iran da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya tare da wasu kungiyoyin Larabawa da na musulmi duk sun yi Allah wadai da kona kur'ani mai tsarki a Sweden, tare da bayyana hakan a matsayin tsokana ga musulmin duniya.

Gwamnatin kasar Sweden ta zargi ‘yan kasashen waje da hannu a al’amuran da suka biyo bayan kona kur’ani mai tsarki da Paludan ya yi.

Ministan shari'a na Sweden Morgan Johansson ya ce Paludan da alama yana neman haddasa rikici da zai cutar da kasar .

Bayan faruwar lamarin, an gudanar da zanga-zanga da dama a kasar Sweden don nuna adawa da wulakanta kur'ani, wanda ya raunata 'yan sanda 26 da masu zanga-zangar 14 tare da lalata motocin 'yan sanda 20.

342/