Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

22 Afirilu 2022

14:15:50
1250644

Rasha Ta Kakabawa Wasu Jami’an Amurka Da Na Canada Takunkumi

Gwamnatin Moscow, ta sanar da kakabawa wasu jami’an gwamnatin Amurka da kuma na Canada takunkumi a matsayin maida martani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Matakin na Rasha ya tanadi haramtawa jami’an Amurkar 29 shiga kasar, da suka hada da ‘yan siyasa, sadarwa da kuma attajirai a matsayin maida martani ga gwamnatin Washington sakamakon takunkuman data kakaba mata saboda farmawa Ukraine.

Daga cikin jami’an na Amurka da takunkumin ya shafa har da Kamala Harris mataimakayar shugaban Amurka, da kuma shugaban kamfanin facebook da ake kira Meta a yau wato Mark Zuckerberg.

Haka kuma Rashar ta haramtawa wasu ‘yan Canada 61 shiga kasar a matsayin maida martani kan irin wanan matakin na mahukuntan Ottawa suka dauka kanta saboda yakin Ukraine.

Jami’an da matakin na Rasha ya shafa sun hada da na gwamnati da kuma sojoji, kuma an haramta musu shiga Rashar har sai abunda hali ya yi, kamar yadda ma’aiakatar harkokin wajen Rashar ta sanar.

342/