Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An cimma yarjejeniyar ce mako guda da ya gabata tsakanin ministocin tsaro na kasashen biyu a birnin Moscow.
Kasashen biyu sun amince musayar bayanai akan siyasar tsaro da kuma tsaro na kasa da kasa, da horon sojoji da dai wasu batutuwa da suka shafi ilimi a harkar soji.
Haka kuma zasuyi musaya ta kwarewa kan tabbatar da zaman lafiya da cudanya a harkar soji a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.
Masana da dama dai sun yaba da matakin na Kamaru na kula irin wanan yarjejeniya a daidai lokacin da kasar Rasha ke shan suka a duniya game da yakin da ta shelanta kan kasar Ukraine, da kuma cece-kucen da ake kan kasancewar sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner a nahiyar ta Afrika.
Kamaru dai na daga cikin kasashen yankin dake fuskantar matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyar boko haram a yankin arewa mai nisa, haka ma tana fama da matsalar tsaro a gabashin kasar mai nasaba da masu fafatukar a ware a yankin masu magana da turancin ingilishi.
342/