Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

21 Afirilu 2022

20:46:03
1250390

Zaben Faransa : An Tafka Muhawara Tsakanin Le Pen Da Macron

‘Yan takaran da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Faransa sun tafka muhawarar keke-da-keke ta gidan talabijin gabanin zaben da za’a gudunar a ranar Lahadi mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Batutuwan da suka mamaye muhawarar ta tsakanin shugaba mai barin gado Emanuel Macron mai ra’ayi tsaka-tsaki da kuma abokiyar hamayarsa mai ra’ayin rikau Marine Le Pen, sun hada da Turai, Rasha, ritaya, nukiliya da lullubi da dai sauransu.

Game da yakin Ukraine, ‘Yar takara Le Pen, ta sake nanata adawarta game da sanya takunkumi kan gas da kuma man fetur na Rasha, tare da zargin turai da mika Rasha ga kasar China, wanda babban hadari ne a cewarta ga faransar da kuma turai.

A game da bayanin ‘yar takara Le Pen ta yi cewa za ta haramta wa mata musulmi sanya lullubi a bainar jama'a, Macron ya ce wannan yunkurin na ta zai haifar da yakin basasa a kasar.

Kimanin ‘yan kasar miliyan 15,6 ne suka kalli muhawarar da aka kwashe kusan sa’a uku anayi tsakanin ‘yan takaran, sabanin kusan mutum miliyan 16,5 da suka kalli irin wannan muhawarar a 2017 data hada Le Pen da Macron.

342/