Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A lokacin da sojojin Rasha su ka killace garin a farkon watan Maris da akwai sojojin Ukiraniya da mayakan sa-kai na Azov, da kuma ‘yan kasashen waje da su ka kai 8,100.
Da akwai sojojin kasar ta Ukiraniya 1,400 da su ka ajiye makamansu da mika kasu ga sojojin Rasha, kamar yadda ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya bayyana.
Ministan tsaron na kasar Rasha ya kuma ce; Ya zuwa yanzu an fitar da fararen hula da su ka kai 142,000 daga cikin garin.
Shugaban kasar Rasha Vlademir Putin ya bukaci ganin an bai wa mayakan da suke cikin masana’antar Azovstal wani wa’adi da su mika kansu, maimakon a kutsa cikinsa.
A gefe daya, minstan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergey Lavrov ya ce; Tattaunawa da kasar Ukiraniya ba za ta ci gaba ba, matukar Kiev ba ta amince da sharuddan Moscow ba.
342/