Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

19 Afirilu 2022

20:03:06
1249728

Rasha Ta Zargi Kasashen Yamma Da Tsawaita Yakin Ukraine

Kasar Rasha ta zargi Amurka da kasashen yamma da tsawaita yaki ta hanyar mikawa Ukraine makamai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake sanar da hakan ministan tsaron Rashar, Sergueï Choïgou, ya kuma bukaci dakarun Kiev, dasu ajiye makamai.

Kafin hakan dai ma’aikatar tsaron Rashar ta sanar yau Talata da kaddamar da gomman hare hare a wasu cibiyoyi da sansanonin soji a gabashin Ukraine a cikin daren jiya.

A nasa bangare Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce zasu ci gaba da jan daga domin kare kasarsu.

342/