Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

18 Afirilu 2022

17:50:06
1249291

​Putin: Kasashen Turai Suna Cutar Da Kansu Ne Ta Hanyar saka Wa Rasha Takunkumi

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, kasashen yammacin duniya sun cutar da kansu ta hanyar kakabawa Rasha takunkumi kan batun Ukraine, yana mai jaddada cewa sun haddasa tabarbarewar tattalin arzikin kasashen yammacin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Putin ya bayyana hakan ne a wani taro kan al'amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki a yau Litinin inda ya ce: "A bayyane yake cewa babban abin da ke haifar da matsalar tattalin arziki a 'yan kwanakin nan shi ne matsin lamba na takunkumi, matsin lamba daga kasashen yammacin Turai, kuma makasudin shi ne rusa kudi da tattalin arzikin Rasha.

Ya kara da cewa kasar Rasha ba kasa ce da za a iya durkusar da tattalin arzikinta cikin sauki ba, domin kuwa tattalin arzikinta yana da alaka da al’ummomin duniya, duk wani abin da zai cutar da Rasha, to tabbas zai cutar da duniya.

Putin ya ce, hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar ta Rasha yana kara daidaita, kuma bukatar da ake da ita na sayar da kayayyaki a cikin kasar komai ya dawo daidai.

Putin ya kara da cewa, ya zama wajibi a ci gaba da sanya ido kan yanayin tattalin arziki da kasuwar kwadago da kuma daukar matakai kan lokaci, yana mai jaddada cewa babban bankin kasar da gwamnati sun yi nasarar yin hakan a kowane lokaci.

Lokaci ne na tabbatar da kwanciyar hankali da kwarin gwiwa a harkokin kasuwanci ga ’yan kasuwa.

342/