Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

18 Afirilu 2022

17:49:19
1249290

​Kasashen Musulmi Na Ci Gaba Da Mayar Da Martani Kan Kona Kur'ani A Sweden

Kasashen Masar da Saudiyya da Iran sun jaddada wajibcin hana cin mutuncin duk wani addini, biyo bayan wulakanta kur'ani mai tsarki da shugaban wata kungiyar masu tsatsauran ra'ayi a kasar Sweden ya yi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya habarta cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da matakin da wasu masu tsattsauran ra’ayi a kasar Sweden suka dauka na keta alfarmar kur’ani mai tsarki da kuma tunzura musulmi da gangan.

A cikin sanarwar, Saudiyya ta jaddada muhimmancin kokarin da ake yi na bunkasa tafarkin tattaunawa, hakuri da zaman tare, yin watsi da kiyayya, tsatsauran ra'ayi, da kawar da kai da hana cin mutuncin dukkan addinai.

Shi ma a nasa bangaren Ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar Mohammed Mukhtar Juma ya rubuta martani kan wannan lamari a shafinsa na Twitter cewa: "Duk wani aiki na tsatsauran ra'ayi da zai kai ga kona Al-Qur'ani mai girma, kyama ce da wariya da ke cutar da dukkanin musulmi, kuma hakan yana haifar da kiyayya ta zamatakewa tsakanin mutane.

Ya ce, Suna cutar da zaman tare. da zaman lafiyar ‘yan Adam da na duniya, don haka ya kamata a guji tozarta addinin wasu, domin hakan babu abin da zai haifar sai rashin zaman lafiya, a kan ya ce suna yin tir da Allawadai da kona kur’ani a Sweden.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin Iran ta fitar da bayania hukuamnce wanda yake yin Allawadai da kakkausar murya kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da masu kyayya da musulunci suka yi a cikin kasar Sweden, tare da bayyana hakan a matsayin wuce gona da iri da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi.

Rasmus Paluden shugaban jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi a kasar Denmark ya kona kur'ani a wata unguwa da ke kasar Sweden, Lamarin dai ya haifar da zanga-zanga a kasar Sweden domin nuna adawa da wulakanta addinin muslunci ta hanyar keta alfarmar kur'ani mai tsarki.

342/