Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

15 Afirilu 2022

14:20:18
1248314

​MDD: An Rufe Makarantu Fiye Da Dubu 11 A Najeriya Saboda Matsalolin Tsaro

Majalisar Dinkin Duniya ta ce makarantu dubu 11, 536 aka rufe a Najeriya tun daga watan Disambar shekarar 2020 saboda fargabar ‘Yan bindigar dake zuwa suna kwashe dalibai suna garkuwa da su, matsalar da tayi matukar illa ga harkar bayar da ilimi ga yara kusa miliyan guda da rabi a shekarar da ta wuce.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar da jami’in Hukumar UNICEF Samuel Kaalu ya gabatar tace dakile ci gaba da karatun ya haifar da gibi wajen baiwa yaran ilimi da kuma fasaha, matsalar da yace zai kaiga asarar kusan Dala biliyan 3 da rabi na abinda ya dace wadannan yara su samu a rayuwar su, wanda zai dada haifar da talauci a tsakanin al’umma.

Kaalu yace UNICEF da taimakon masu bada agaji na hadin kai da gwamnatin Najeriya wajen kare hakkokin yara na samun ilimi a yankunan dake da cikakken tsaro a karkashin shirin da ya kunshi horar da malamai akan yadda zasu tabbatar da tsaron daliban su da kuma hadin kan jama’a.

UNICEF ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara daukar matakan tsaro domin kare makarantu da kuma baiwa yara kariyar da suke bukata na samun ilimi, musamman yara mata.

Sanarwar UNICEF ta bayyana cewar harin farko da aka samu a Najeriya shine na makarantar sakandaren yammata na Chibok a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, inda mayakan boko haram suka kwashe dalibai 276.

UNICEF tace tun daga wancan lokaci an samu karuwar kwashe dalibai a makarantu daban daban, abinda ke kaiga rasa rayuka a wasu lokuta, matsalar da ta yadu daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Sanarwar tace daga watan Disambar shekarar 2020 zuwa yanzu, dalibai 1,436 da malamai 17 aka sace a makarantu daban daban, kuma dalibai 16 daga cikin su sun rasa rayukan su.

342/