Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Jummaʼa

15 Afirilu 2022

14:11:41
1248306

Labarai Cikin Hotuna / Na Taron Shekara - Shekara Na Tunawa Da Wafatin Sayyida Khadijeh (a.s) Tare Da Halartar Waakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo labarin cewa, ofishin wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iraki ya gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar rasuwar Sayyida Khadijeh (a.s) tare da halartar daruruwan malamai da sauran bangarori mutane, in da aka gundanar da shi a makarantar hauza ta Imam Khumaini da ke Najaf Ashraf. A cikin wannan taro an fara da gabatar da karatun Qari Karim Mansouri na kasa da kasa, sai kuma Ayatullah Sayyid Mojtaba Hosseini wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya yi tsokaci kan kyawawan halaye na Sayyida Khadija (AS).