Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

14 Afirilu 2022

14:02:32
1248016

Tedros : Ba'a Yi Wa Bakake Adalci Wajen Gudanar Da Ayyukan Jinkai

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya zargi kasashen duniya kan yadda suke nuna banbanci dangane da rayukan bakaken fata da farare wajen gudanar da ayyukan jinkai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gebreyesus, ya lura da abin da ke faruwa a kasar Ukraine, da kasar Rashar ta abkawa da yaki. M. Gebreyesus ya ce irin yadda kasashen suka mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan jin kai a Ukraine ya saba da yadda ake gudanar da su a wasu sassan duniya musamman idan matsalar ta shafi bakaken fata. Shugaban Hukumar ta WHO, ya ce yana da kyau irin yadda ake kaiwa Ukraine dauki saboda yadda rikicin kasar ke yi wa kasashen duniya illa, amma kuma matakin ya ribanya yadda ake yiwa Yankin Tigray da Yemen da Syria da Afghanistan da kuma wasu yankunan duniya. Gebreyesus ya ce ya zama wajibi ya bayyana gaskiyar abinda ke faruwa akan yadda duniya bata dauki mutane a matsayin abu guda ba.

342/