Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Laraba

13 Afirilu 2022

21:54:31
1247760

Labarai Cikin Hotuna / Na Asarorin Da Aka Samu A Fashewar Abubuwa A Sidon

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo labarin cewa, an samu fashewar wani abu a safiyar jiya Talata a kusa da daya daga cikin hedkwatar kungiyar Amal da ke birnin Sidon a kudancin kasar Lebanon. Wasu majiyoyi sun ce wurin da tashin bam din ya faru, wata ma'ajiyar harsashi ce ta kungiyar Amal, yayin da wasu ke cewa ginin farar hula na kungiyar ya tarwatse. Fashewar ta lalata wani gini na karamar hukumar da kuma wani gini dake kusa da kudancin Sidon. A cikin wannan lamari dai an kashe Ali Tawfiq Al-Raz dan hakimin gundumar Benaful tare da jikkata wasu 7.