Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

13 Afirilu 2022

17:07:57
1247739

. Rasha Ta Bayyana Aniyarta Ta Yin Aiki Tare Da Iran A Fagen Hada Magunguna

Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Rasha Mikhail Murashko ya bayyana cewa; Iran ta sami ci gaba a fagen yin magunguna, don haka muna son yin aikin hadin gwiwa da ita a wannan fagen.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan kiwon lafiyar na Rasha ya kuma ce; A lokaci mai tsawo da akwai tuntubar juna a tsakaninmu da takwarorinmu Iranawa, kuma zai ci gaba.

Mikhail Murashko ya kawo ziyarar aiki ne a Iran, inda ya gana da jami’an ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran.

342/