Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Laraba

13 Afirilu 2022

17:03:15
1247734

Rasha Da Belarus Za Su Kara Karfafa Alakarsu Domin Dakile Takunkumin Kasashen Yamma

Kasashen Rasha da Belarus, sun kudiri anniyar karfafa cudanyar tattalin arziki dake a tsakaninsu.

Wannan bayyanin ya fito ne yayin taron manema labarai da shugabannin kasashen biyu suka gudanar, yayin ziyarar shugaban Belarus Alexander Lukashenko a Rasha.

Shugaba Putin ya bayyana cewa, kasarsa da Belarus za su kara karfafa cudanyar tattalin arzikin dake tsakaninsu, ta yadda za su dakile takunkumin da kasashen yamma suke kakaba musu, kana ya ce kasar Belarus, dandali ne mai dacewa ga Rasha na yin shawarwari da Ukraine.

A nasa bangaren, shugaba Lukashenko ya bayyana cewa, kasar Amurka tana shawo kan Ukraine, da Poland, da kasashe uku dake gabar tekun Baltic, wato Estonia, da Latvia, da Lithuania, domin su yaki Belarus, don haka Belarus din za ta hana duk wata dama ta yakar Rasha, yayin da kasar ke gudanar da aikin soji na musamman.

342/