Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

10 Afirilu 2022

20:29:50
1246837

Ana Zaben Shugaban Kasa A Faransa

A Faransa yau Lahadi ne al’ummar kasar suke kada kuri’a a zagaye na farko na zaben shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Masu kada kuri’a miliyan 48,7 aka tantance za su je rumfunan zaben, wanda ake da fargaba akan fitowar jama’a sosai a yayinsa.

Yan takara 12 ne dai ke neman kujerar amma takarar ta fi zafi tsakanin mutum uku.

'Yan takarar uku dai su ne shugaba mai barin gado Emmanuel Macron da Marine le Pen da Jean Luc Melenchon.

Zai yi wuya dai a samu mutumin da sai samu gagarimun rinjaye a farat daya saboda haka sai an kai ga zagaye na biyu na zaben a ranar 24 ga watan Afrilu.

Da misalin karfe takwas na daren yau ne ake sa ran samun sakamakon zaben.

342/