Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

9 Afirilu 2022

15:02:02
1246458

FAO : Farashin Abinci Ya Yi Mugun Tashi Sakamakon Yakin Ukraine

Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD, ta ce an samu hauhawan farashin kayan abinci da man girki wanda ba’a taba ganin irinsa ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A rahoton da ta fitar hukumar ta FAO, ta ce farashin alkama, shinkafa, masara da dangoginsu da man girki sun ya yi mugun tashi a kasuwanin duniya a watan Maris da ya gabata sakamakon yakin Ukraine.

Rahoton ya ce yakin na Rasha da Ukraine kasashe biyu mafi fitar da albarkatun gona a duniya ya sanya farashin abincin ya karu daga kashi 12,6 cikin dari daga watan fabarairu zuwa 17,1 a watan Maris.

Har yanzu da saura a tsira daga lamarin duba da yadda har yanzu ba’a san ranar kawo karshen rikicin ba a cewar rahoton na FAO.

Hakazalika hakan babbar barazana ce ga makomar noma a nan gaba a cewar Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD.

342/