Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Laraba

6 Afirilu 2022

12:31:39
1245484

Tunusiya Ta ce: “ Ba Za ta Amince Da Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidanta Da Kasar Turkiya Ta yi Ba

Ministan harkokin wajen kasar Tunusiya ya fadi cewa kalaman da shugaban kasar Turkiya Dayyib rajab Ardogan yayi game da rusa majalisar dokokin kasar da aka yi a makon jiya shiga sharo ba shanu ne cikin harkokin cikin gidanta kuma za’a amince da shi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya ne shugaban kasar Turkiya Dayyib Rajab Ardogan yayi suka game da matakin da shugaban kasar Tunusiya Kais Saed ya dauka na rusa majalalisar dokokin kasar tare da bayyana shi a matsayin cin amanar Demukuradiya da kuma sabawa muradun alummar kasar

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Tunusiya ta nuna bacin ranta game da wadanan kalamai kuma ta ce ba za ta amince da su ba, yace duk da kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da kasar Turkiya amma tana da yanci akan ra’ayinta kuma tayi tir da duk wani mataki na yin katsalandam a cikin harkokin mulkin kasar

A makon jiya ne wani rikicin siyasa ya kara kunno kai a kasar bayan da mafiyawancin yan majalisar kasar suka kira taro daga Nesa domin karya dokar da shugaban kasar ya saka, wannan yasa shugaban kasar ya sanar da rusa majalisar baki daya .

342/