Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

6 Afirilu 2022

12:29:27
1245482

Kunagiyar Tarayyar Turai Ta Bukaci A Sake Kakabawa Kasar Rasha Wasu Sabbin Takunkumi

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta bukaci a sake kakabawa kasar Rasha wasu sabbin takunkumi saboda harin soji da ta kaddamar kasar Ukrain adaidai lokacin da aka samu sabanin tsakanin shawagabannin kasashen kungiyar game da batun kara matsin lamba kan kasar Rasha kan makamashi da take shigarwa yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kungiyar ta Eu ta bukaci a hana kasar Rasha shigar da Coal da kuma hana jiragen ruwa na kasar rasha shiga gabar ruwan kasashen kungiyar, kuma ana ganin idan kudurin ya samu amincewa zai shafi hanata shigar da man jirgin sama karfe da sauran kayyakakin jin dadi.

Sai dai har yanzu kan shuwagabannin kasashen turai din ya rabu gida biyu tsakanin wadanda ke ganin a fadada takunkumin yadda zai shafi siyan makamashinta inda suka cikin matsin lamba na dakatar da siyan makashi daga hannunta , sai dai kasahen Jamus da Austeriya da italiya da suka dora baki daya wajen samar da makamashi daga kasar Rasha suna taka tsantsan game da shigar da takunkumin ya shafi manfetur ko kuma Iskar Gas.

Kasashen turai sun kakabawa kasar Rasha takunkumi tun bayan da hshugabn kasar Viladmir Putin ya shelanta kai harin soji kan kasar Ukrain a ranar 24 ga watan Fabareru.

342/