Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

5 Afirilu 2022

19:11:45
1245177

Kasashen Turai Suna Ci Gaba Da Koran Jami’an Diplomasiyyar Kasar Rasha

Daga cikin kasashen da su ka kori adadi mai yawa na jami’an diplomasiyyar kasar Rasha da akwai Jamus, Faransa, Lithuania, bisa zargin da ake yi na cewa sojojin Rashan sun yi kisan kiyashi a garin Bucha na kasar Ukarania.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministar harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock ta sanar a jiya Litinin cewa; kasarta za ta kori adadi mai yawa na jami’an diplomasiyyar Rasha saboda yakin da take yi da kasar Ukirania.

Ministar harkokin wajen kasar ta Jamus ta ci gaba da cewa; Adadin jami’an diplomasiyyar da za a kora za su kai 40, domin suna a matsayin barazana ne ga wadanda su ke neman mafaka a wurinmu.

Jamus ta bai wa jami’an diplomasiyyar Rasha din kwanaki biyar da su fice daga kasar saboda zarginsu da ake yi da aikin leken asiri.

Ita kuwa kasar Lithuania ta sanar da korar jakadan kasar Rasha ne. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Lithuania ta sanar da cewa; Saboda yakin da sojojin Rasha su ke yi da Ukirania wacce kasa ce mai ‘yanci, musamman a garin Bucha, gwamnati ta yanke hukunci korar jakadan Rasha.

A can birnin Moscow, ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ce za ta mayar da martani mai tsanani akan matakin na kasashen turai.

342/