Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

3 Afirilu 2022

20:26:25
1244486

Wani Abun Fashewa Mai Kara Ya Girgiza Birnin Baku Na Kasar Azarbaijan

Rahotanni dake fitowa daga jamhuriyar Azarbaijan sun nuna cewa da sanyi safiyar yau lahadi ce aka ji karar fashewar wani abu mai tsananin kara a wani waje dake babban birnin Baku fadar mulkin kasar da hakan yayi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma’aikatar lafiyar kasar Azarbaijan ta sanar cewa kimanin mutane 24 ne suka jikkata ciki har da mutane 13 da wasu mata 11 sakamakon konewa da suka yi inda tuni aka kais u Asibiti domin yi masu magani,

Yace an aike da motocin daukar marasa lafiya fye da 35 da kuma tawagar masu bada agaji da yawa domin ayyukan a gaji a wajen.

Majiyar jami’an tsaron kasar ta Azarbaijan ta fadi cewa yazuwa yanzu an shawo kan al’amura kuma an kashe gobarar da ta tashi

A wani faifan video da aka yada ya nuna yadda mutane suke ihu suna ficewa a waje da gudu daga cikin gini , fashewar ta tunkunyar gas ne ya haddasa afkuwar lamarin.

342/