Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

3 Afirilu 2022

20:18:27
1244478

​Rasha Ta Bayyana Damuwa Kan Karuwar Ayyukan ‘Yan Ta’adda A Tsakiya Asia

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana damuwarsa kan shirin kungiyar ISIS na kara yawan ayyukanta da kuma fadada ta'addanci zuwa kasashen tsakiyar Asiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - "Moscow ta damu da shirin kungiyar ta'addanci ta ISIS na kara rashin zaman lafiya da kuma fadada ta'addanci zuwa tsakiyar Asiya da Rasha."

Lavrov ya ce, "Muna matukar damuwa da shirin kungiyar da masu alaka da su na tada zaune tsaye a tsakiyar Asiya da kuma yada rashin zaman lafiya a kasar Rasha," in ji Lavrov a babban taron koli na makwaftan Afghanistan.

Har ila yau ya bayyana damuwarsa game da yadda dakarun kungiyar ta ISIS suka taru a kusa da kan iyakokin kasashen Afghanistan, Tajikistan, Uzbekistan da suke makwabtaka da Afghanistan.

Ministan harkokin wajen Rasha ya je kasar Sin domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen da ke makwabtaka da Afghanistan da tawagar Taliban.

Da yawa daga cikin al'ummomin kasashen tsakiyar Asiya, musamman 'yan kasar Uzbekistan da Tajikistan, na sha'awar shiga kungiyar ta'addanci ta Da'ish tare da shiga mayakan kungiyar ta'addancin a ke Siriya musamman ta hanyar Turkiyya. Haka kuma wasu da dama daga cikinsu na da hannu a ayyukan wannan kungiyar ta'addanci a kasar ta Afganistan.

Sakamakon fatattakar 'yan ta'addar Da'esh a Siriya da Iraki, da kuma faduwar gwamnatin Afganistan da ke samun goyon bayan kasashen Yamma, da sake bullowar 'yan Taliban a wannan kasa, damuwar da ake ciki a kasashen da ke makwabtaka da Afganistan na kara ta'azzara game da mayar da kasar wani sansani na ayyukan ISIS.

342/