Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

3 Afirilu 2022

20:14:23
1244474

​Antonio Guterres Ya Taya Musulmi Murna Shiga Wata Ramadan

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya taya musulmin duniya murnar shigowar watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin sakon nasa a cikin wani faifan bidiyo ya ce, “Ina yi wa Musulman duniya da suka fara azumin watan Ramadan fatan alheri.”

Ya kara da cewa, “Ramadan wata ne na kyautatawa, tunani da ilmantarwa, kuma wata dama ce ta haduwa da inganta alaka da juna da kuma nuna tausayawa ga masu rauni da mabukata.

A cikin sakon bidiyo na Guterres ya ce "a cikin Kowane watan Ramadan, ina samun karramawa na yin balaguro zuwa kasashen Musulunci da kuma yin azumi don nuna goyon baya ga musulmi da kuma buda baki tare da al’ummomin musulmi a kasashe daban-daban.."

Ya kara da cewa "Abin takaici, annobar korona ta sa hakan ba zai yiwu ba, amma ina farin cikin samun damar dawo da wannan irin yanayi a wannan shekara," in ji shi.

“A cikin wadannan kwanaki na kunci da wahala, hankalina da zuciyata suna tare da duk wanda ke cikin kunci da fargaba saboda matsaloli na yaki ko gudun hijira da makamantan haka.

Ya yi ishara da aya ta 13 a cikin suratu Hujurat, inda ya yi karin bayani kan ayar da cewa “Allah ya halicce mu ne da sigar mata da maza a cikin kabila da al’ummomi domin mu san juna mu fahimci junanmua cikin rayuwa, Mu yi koyi da juna, mu gina rayuwa ta zama lafiya a tare," in ji Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

342/