Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

2 Afirilu 2022

11:22:28
1243926

Rasha : Putin Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tilastawa Kasashen Turai Biyan Gas Da Kudin Ruble

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya sanya hannu kan dokar tilastawa kasashen turai biyan kudin gas da suke saye da kudin Rasha na Rouble.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wani jawabi ta bidiyo jiya shugaba Putin, ya yi gargadin cewa kasarsa za ta daina sayar da iskar gas ga kasashen Turai daga ranar yau Juma'a, sai idan kasashen sun amince su fara biyan kudin gas din da takardar kudi ta Rouble.

Dokar a cewar Mista Putin za ta fayyace tsarin kasuwanci da kasashen da ya ambata da wadanda ba amintatu ba ne.

Ya ce ya dauki matakin ne saboda kasashen yamma na amfani da tsarin kasuwancin a matsayin makami, saboda haka babu dalilin da zai sa Rasha ta ci gaba da amfani da takardun kudaden kasashen waje.

Tuni dai kasashen Jamus da Faransa da Austria suka yi watsi da bukatun na Putin.

342/