Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

30 Maris 2022

14:51:48
1243157

Rasha Za Ta Rage Ayyukan Sojinta A Kiev da Chernihiv

Kasar Rasha ta sanar cewa za ta rage ayyukan sojinta a Ukraine, musamman a yankunan Kiev da Chernihiv.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha da ake kira TASS, ya rawaito ma'aikatar tsaron kasar na cewa, ta yanke shawarar rage yawan ayyukan soji a yankunan guda biyu na Kiev da Chernihiv.

Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar neman sulhun da kasashen biyu sukayi a Turkiyya jiya Talata.

Jagoran tawagar kasar Rasha a tattaunawar, Vladimir Medinsky, ya bayyana a ranar cewa, kasar ta karbi shawarwarin da Ukraine ta gabatar mata a rubuce, inda ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da kasancewa tsaka-tsaki, da matsayin da bai shafi nukuliya ba.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Rasha ba ta adawa da shigar kasar Ukraine cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Kafin nan hukumomin Turkiyya da kafofin yada labarai sun bayyana tattaunawar da mai armashi.

Wakilin Ukraine a tattaunawar ya ce matsayin da aka cimma kawo yanzu zai iya bada damar ganawa ta kud da kud tsakanin Volodymir Zelensky da kum Vladimir Putin.

342/