Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

30 Maris 2022

14:44:01
1243148

Rasha Ta Sanar Da Rage Yawan Wasu Hare-haren Da Take Kai Wa A Ukireniya

Ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa za a rage yawan harin da ake kai wa birnin Qif ta hanyar garin Chernihiv, domin bayar da damar tattaunawar diplomasiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mataimakin ministan tsaron kasar ta Rasha Alexander Fomin wanda ya halarci tattaunawar da kasr Ukireniya da ake yi a birnin Istanbul na kasar Turkiya, ya ce; Bisa la’akari da ci gaban da ake samu na tattaunawa akan zaman kasar Ukireniya ‘yar ba-ruwanmu, da kwance damararta ta makaman Nukiliya, Rasha ta yanke rage yawan hare-haren da take kai wa babban birnin kasar ta hanyar garin Chernihiv.

Fomin ya ci gaba da cewa; Daukar wannan matakin na rage hare-haren da ake kai wa yana nufi samar da kwarin gwiwa ne akan tattaunawar da take ci gaba domin cimma manufofi na karshe.

Shugaban tawagar kasar Rasha a wurin tattaunawar Vladimir Medinsky ya ce; Tattaunawar ta yi armashi, kuma za a mikawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin rahoto, za kuma a shigar da abubuwan da aka tattauna a cikin yarjejeniyar da da ake son kullawa anan gaba.

Abubuwan da Rasha take bukata daga Ukireniya su ne; Ta zama ‘yar baruwanmu ba tare da ta shiga cikin wata kungiya ta yarjejeniyar tsaro ba, kamar Nato, ta kuma rage yawan sojojinta zuwa 50 kawai, sannan kart a yi tunanin kera makaman Nukiliya anan gaba.

342/