Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

25 Maris 2022

21:18:51
1242359

​Ukrain: Kasashen Yamma Sun Kara Takurawa Kasar Rasha Kan Yaki A Ukrain

Kasar Amurka da kawayenta sun tsaida shawarar kara takurawa kasar Rasha saboda yakin da take fafatawa da sojojin Ukrain.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jens Stoltenberg babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO yana fadar haka bayan an kammala taron kungiyar a birnin Brussels na kasar Beljium.

Daga cikin matakan da zasu dauka dai akwai aike da sojojinsu zuwa kasashen NATO na gabacin Turai, kara tura makamai zuwa kasar Ukrain da kuma kara tsananta takunkuman tattalin arziki kan kasar Rasha.

A jiya Alhamis ne aka gudanar da tarurruka kungiyoyi guda uku a kasar ta Beljium dangane da kasar Rasha. Kuma sun hada da NATO, G& da kuma EU.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu akwai sojojin NATO a kalla dubu 10 a gabacin Turai kuma zata kafa wasu karin sansanonin soje a kasar Bulgaria, Romania, Hungary da Slovakia. Banda haka NATO ta ce ta shiryawa hare-hare mafi muni a kasashen gabacin turai, na makaman guba, nukliya da kuma cututtuka.

Jamus tana aike da makaman wargaza tankunan yaki 2000, zuwa Ukrai sannan Burtaniya ta aika da makamai masu linzami 6000 zuwa kasar ta Ukrain.

342/