Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

22 Maris 2022

18:19:32
1241641

Batun Sanyawa Rasha Takunkumi Kan Man Fetur Ya Raba Kan (EU)

A wannan mako ne ake sa ran kasashen yamma zasu sake wani taro domin nazarin kakabawa Rasha takunkumi kan gabadayen man fetur dinta da iskar gas.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Saidai wannan batun na ci gaba da kawo rarrabuwar kai tsakanin kasashe 27 mambobin kungiyar (EU), a daidai lokacin da farashin man fetur ke kara tashi a duniya.

Kasashen tsakiyar turai su ne dai wadanda suka fi damuwa game da batun sanya wa Rashar takunkumi, duba da yadda dayewa daga cikinsu suka dogara da makamshin Rasha.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Ukraine ke shiga kara shiga halin rashin tabbas.

342/