Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - WHO, ta ce ba ta ji daidin wannan matakin ba da Kasashen turan da dama ne da suka hada da Jamus, Faransa, Italiya da kuma Biritaniya suka dauka ba tare da wani shiri ba, a daidai lokacin da kuma suka fara fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar karamin nau’in BA.2
Yayin wani taron manema labarai a Moldavie, darektan hukumar ta WHO, rashen turai, Hans Kluge, ya su ne bibiyar halin da ake ciki a nahiyar.
A halin da ake ciki dai yawan masu kamuwa da cutar ta korona ya karu a kasashe 18 daga cikin 53 na yankin a cewar WHO.
342/