Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

22 Maris 2022

18:16:08
1241637

​MDD Ta Ce An Kashe Fararen Hula 925 A Yakin Ukrain Ya Zuwa Yanzu

MDD ta bada sanarwan cewa ya zuwa yanzu ta sami rahoton mutuwar fararen hula 925 a yakin da ake fafatawa da sojojin Rasha a kasar Ukrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto ofishin hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar (OHCHR) yana fadar haka a jiya litinin a wani rahoton da ta fitar.

Labarin ya kara da cewa tabbas fararen hula wadanda suka rasa rayukansu tun bayan da sojojin Rasha suka farwa kasar Ukrain da yaki a ranar 24 ga watan Fabraini na wannan shekarar ta 2022 ya dara wannan adadin nesa ba kusa ba.

Wannan saboda har yanzun ba’a sami kalumman wadanda aka kashe ko suka ji rauni a yankunan da ake fafatawa ba.

Banda haka labarin ya ce fararen hula 1,496 ne suka ji raunin sanadiyyar yakin ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata . Kuma ana ci gaba da yaki a sassa daban –daban na kasar.

342/