Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Maris 2022

22:37:54
1241367

​Alexander Novak : Takukunkumin EU Kan Man Rasha Zai Iya Tayar Da Farashin Mai Zuwa $300 A Kan Ganga

Mataimakin firaministan kasar Rasha Alexander Novak ya yi gargadi kan illar takunkumin hana shigo da mai na Rasha daga bangaren Tarayayr Turai, inda ya ce farashin mai zai kaiwa dalar Amurka 300 kan ganga guda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar ta Novak ta zo ne a wani taro da aka gudanar a yau Litinin, tare da wakilan jam'iyyar "United Russia" inda aka tattauna halin da ake ciki a kasuwar mai ta Rasha.

Mataimakin firaministan na Rasha ya ce kin amincewa da iskar gas na Rasha daga bangaren Turai ba zai taba yiwuwa ba a halin yanzu.

Kuma idan kasashen Yamma suka ki amincewa da man kasar Rasha, to farashin zai tashi zuwa dala 300, yayin da wasu ke ganin yiwuwar tashin gangar mai har zuwa dala 500."

342/