Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Maris 2022

22:37:12
1241366

​Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Na Neman A Tsagaita Wuta A Yemen

Ofishin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen ya ce, ana binciken yiwuwar dakatar da bude wuta a kasar a cikin watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar ofishin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen Hans Grundberg, jami’in ya gana da babban mai shiga tsakani na kungiyar Ansarullah da jami'an gwamnatin kasar Omani a birnin Muscat a ranar Asabar da ta gabata.

Makasudin taron dai shi ne tattauna shawarwarin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a baya-bayan nan da kuma kokarin shawo kan mummunan halin da ake ciki a kasar Yemen.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya ce taron nasu ya mayar da hankali ne kan aiwatar da shirin tsagaita wuta a cikin watan Ramadan da kuma ci gaba da tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa.

Rikicin Yemen ya haifar yanayi mafi muni a duniya, kuma a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan kashi 80 cikin 100 na mutanen kasar Yemen, wato kimanin mutane miliyan 30 a kasar, na bukatar taimako, yayin da fiye da miliyan 13 daga cikinsu kuma suna cikin hadari na yunwa.

Al’ummar kasar Yemen ta fada cikin wanann yanayin ne tun bayan da kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan kan kasar a cikin shekarar 2015 da sunan yaki da mayakan Alhuthi da ba su shiri da ita.

342/