Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Maris 2022

22:34:00
1241362

Gwamnatin Kasar Rasha Ta Bawa Kasar Ukrain Wa’adi Da Ta Mika Wuya A Birnin Mariupol Dake Gabar Teku.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar Rasha ta dibarwa kasar Ukrain wa’adi na ta mika kai da gaggawa a Moriupol , ta yi gargadin cewa yanki bakin teku dake kudu maso gabashin kasar yana fuskantar mummuna bala’I jin kai

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kanar janar Mikhail Mizintsev daraktan cibiyar kula da tsaron kasa na kasar rasha ya fadi cewa yana kira da sojojin Ukrain da su ajiye makamansu , duk wanda ya mika wuya a ajiye makaminsa to za’a bashi lamunin ficewa daga garin na Mariupol domin ana fuskantar mummaun bala’in bukatar agajin gaggawa saboda mawuyacin hali da mutane ke ciki.

An sa bangaren mataimakin fira ministan kasar Ukrain Irina Vereschuku ya sanar da yin watsi da wa’adin da aka rasha ta dibar musu, babu Magana game da batun mika wuya, da kuma ajiye makamai, kuma tuni mun sanarwa da bangaren rasha game da wannan batun

Kasar rasha ta fadi cewa harin da dakarun kasar Ukrain suka kai a yankin Donetsk yayi sanadiyar mutuwar mutane 23, kuma ana zargin sojojin gwamnatin Kiev da tafka laifukan yaki, sai dai mahukumta ukran din sun musanta wannan zargin.

342/