Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

20 Maris 2022

22:12:46
1241140

Ramaphosa : Ba Zamu Kyamaci Rasha Ba Saboda Rikicin Ukraine

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce sake kutsawar kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin Turai ne ya haddasa barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, kuma NATO ba ta fahimci illar da matakinta zai haifar, wanda ya hada da tayar da rikici.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewarsa, ko da yake wasu suna yunkurin rura wuta tsakanin Afrika ta kudu da Rasha, amma kasar ba za ta dauki duk wani mataki na shiga takun tsaka da Rasha ba, yana mai fatan bangarorin biyu da rikicin ya shafa, za su warware bambancin ra’ayi ta komawa teburin shawarwari, saboda yaki da nuna karfin tuwo ba za su yi wani amfani ba wajen warware matsaloli da ake fama da su.

Ban da wannnan kuma, ya ce ba wanda yake son ganin abin da ya faru a Ukraine.

Shi ya sa ake ta fatan a ga an yi sulhu, da komawa shawarwari tsakanin bangarorin da rikici ya shafa.

342/