Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

20 Maris 2022

22:07:43
1241133

​Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Kifewar kwale-kawle A Tekun Medeteranian Ya kai 20

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar kifewar kwale-kwalen da yake dauke da su daga gabar tekun Tunisia kan hanyarsu zuwa kasar Italia ya kai 20.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa jami’an tsari nab akin ruwa a kasar Tunisia sun gano gawakin mutane 12 a jiya Asabar, kafin haka a ranar Jumma’a sun gawaki 12. Mafi yawan wadanda abin ya rusta da su dai yan kasar Siriya ne.

Labarin ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da neman wasu gawakin.

A cikin ‘yan watannin da suka gabata dai ana samun wadanda suke kokarin tsallaka tekun Medeteranian daga kasashen Tuniya da Libya zuwa kasashen Turai musamman kasar Italiya, inda sau da dama sukan halaka a cikin Tekun.

Dubban daruruwan mutane ne daga kasashen Afirka da wasu kasashen da ake yaki ko talauci a kasashensu, suke kokarin rsatwa ta tekeun, amma kuma suke rasa rayukansu a cikinsa. Kasar Italiya ce tafi saukin tsallawa zuwa kasashen na Turai da sauran kasashen.

342/